Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 12:6-35 in Hausa

Help us?

Luka 12:6-35 in Litafi Mai-tsarki

6 Ba a kan sayar da 'yan tsuntsaye biyar a kan anini biyu ba? Duk da haka, Allah ba zai manta da ko daya daga cikinsu ba.
7 Har ma gashin da ke kan ku ya san yawan su. Kada ku ji tsoro, ku kun fi tsuntsaye daraja a wurinsa.
8 Ina gaya maku, dukan wanda za ya shaida ni a gaban mutane, Dan Mutum kuma za ya shaida shi a gaban mala'kun Allah.
9 Kuma dukan wanda ya ki ni a gaban mutane, za a ki shi a gaban mala'ikun Allah.
10 Dukan wanda ya yi magana gaba da Dan Mutum, za a gafarta masa. Amma shi wanda ya yi sabon Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.
11 Idan suka kawo ku gaban majami'a, ko gaban masu shari'a, ko gaban masu iko, kada ku damu da abin da za ku fada domin ku kare kanku. Ko kuwa abin da za ku ce.
12 Gama Ruhu Mai Tsarki zai koya maku abin da za ku fadi a wannan lokaci.”
13 Sai wani a cikin taron ya ce masa, “Malam, ka yi wa dan'uwana magana ya raba gado da ni
14 Yesu ya ce masa, “Kai, wanene ya sa ni in zama alkali, ko matsakanci a kanku?”
15 Sai kuma ya ce masu, “Ku yi lura kada ku zama masu hadama, gama ba abin da mutum ya mallaka ne ya fi mahimmanci a cikin rayuwar sa ba.”
16 Sa'annan Yesu ya fada masu wani misali, ya ce, “Gonar wani mutum ta bada amfani sosai,
17 ya yi tunani, ya ce, 'Me zan yi, domin ba ni da wurin da zan iya ajjiye amfanin gonata?'
18 Sai ya ce, na san abin da zan yi. Zan rushe rumbuna na in gina wadansu manya-manya, a nan zan ajjiye hatsi na da dukan abubuwa.
19 Sai in ce da raina, “Ya raina, kana da abu da yawa da aka ajjiye dominka, sai ka huta, ka ci, ka sha, ka yi murna.”
20 Amma sai Allah ya ce da shi, 'Wawan mutum, a cikin daren nan ana son ranka daga wurinka. Kayan da ka tara ka shirya wa kanka, na wa za su zama?'
21 Haka wanda ya tara wa kansa dukiya yake, idan ba shi da dukiya a wurin Allah.”
22 Yesu, ya ce da almajiransa, “Saboda haka ina cewa da ku, kada ku damu da rayuwarku, wato, abin da za ku ci, ko abin da za ku sa a jikinku.
23 Gama rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.
24 Ku dubi hankaki wadanda ba sa yin shuka, ba sa yin girbi. Ba su da rumbuna ko dakunan ajjiya, amma Allah ya na ciyar da su. Ku fa kun fi tsuntsaye daraja!
25 Wanene a cikinku ta wurin sha'awarsa za ya iya karawa kansa kwanaki?
26 Idan ba ku iya yi wa kanku dan karamin abu ba, me ya sa za ku damu da sauran abubuwa?
27 Ku dubi furanni a daji - yadda suke yin girma. Ba su kan yi aiki ba, ba su kan yi kadi ba. Ina gaya maku, ko Sulaimanu, a cikin darajarsa, bai sa tufafin da suka fi nasu kyau ba.
28 Idan Allah ya sa wa ciyawa tufafi masu kyau haka, wadda yau tana nan, gobe kuma a sa ta a wuta, ta yaya zai kasa sa maku tufafi, ku masu kankantar bangaskiya!
29 Kada ku damu da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kuma kada ku yi alhini.
30 Gama dukan al'umman duniya suna neman wadannan abubuwa, kuma Ubanku ya san kuna bukatar wada nan abubuwan.
31 Amma ku bidi mulkinsa, wadannan abubuwa kuma za a kara maku su.
32 Kada ku ji tsoro, ku 'yan kanana, domin da murna Ubanku zai ba ku mulkin.
33 Ku sayar da abin da ku ke da shi ku ba matalauta. Kuyi wa kanku jakukkuna wadanda ba za su lalace ba, ku yi ajjiya cikin sama inda abin ba ya karewa, inda barayi ba za su iya zuwa ba, kwari kuma ba za su iya lalatawa ba.
34 Domin inda dukiyarka take, can zuciyarka za ta kasance kuma.
35 Ku rage tsawon tufafinku, ku yi dammara, ya zama fitilarku tana ci koyaushe,
Luka 12 in Litafi Mai-tsarki