Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 12:48-57 in Hausa

Help us?

Luka 12:48-57 in Litafi Mai-tsarki

48 Amma shi wanda bai sani ba, kuma yayi abin da ba daidai ba, ba zai sha duka da bulala da yawa ba. Dukan wanda aka ba abu da yawa, za a kuma nemi abu da yawa daga wurinsa. Kuma ga wanda aka ba abu da yawa amana, za a nemi abu mafi yawa daga gareshi.
49 Na zo domin in sa wuta a duniya, na so da ta riga ta kama.
50 Amma ni, ina da baftisma wadda za a yi mani baftisma da ita, kuma na kagara, da an riga an yi ta!
51 Kuna zaton na zo duniya domin in kawo salama? Na ce maku a'a, amma tsattsaguwa.
52 Daga yanzu za a sami mutane biyar a cikin gida daya, kuma za su rarrabu, mutane uku suna gaba da biyu, biyun kuma suna gaba da ukun.
53 Da da mahaifi za su yi gaba da juna, dan zai yi gaba da mahaifinsa. Mahaifiya za ta yi gaba da diyarta, diya kuma gaba da mahafiyarta; uwar miji za ta yi gaba da matar danta, matar da kuma gaba da uwar mijinta.”
54 Yesu, ya kuma gaya wa taron, “Da kun ga hadari ya taso daga yamma, nan da nan sai ku ce za a yi ruwa, haka kuwa ya kan zama.
55 Idan iska tana busowa daga kudu sai ku ce za a yi zafi mai tsanani, haka kuwa ya kan faru.
56 Munafukai, kun iya fasarta yanayin kasa da sama, amma baku iya fasarta abin da yake faruwa yanzu ba?
57 Me ya sa ba ku iya gane abin da zai tamake ku?
Luka 12 in Litafi Mai-tsarki