Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 11:8-12 in Hausa

Help us?

Luka 11:8-12 in Litafi Mai-tsarki

8 Na fada maku, ko da bai tashi ya ba ka gurasar ba, a matsayin abokinsa, ba ka ji kunya ba, ka nace da rokonsa, za ya tashi ya ba ka dukan yawan gurasar da kake bukata.
9 Ni kuma ina ce maku, ku roka za a ba ku; ku nema za ku samu; ku kwankwasa za a bude maku.
10 Domin dukan wanda yake roko ya na karba; dukan wanda ya ke nema kuma yana samu; kuma wanda yake kwankwasawa, za a bude masa.
11 Wanne uba ne a cikinku, idan dansa ya tambaye shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon kifi?
12 Ko kuwa idan ya tambaye shi kwai, za ya ba shi kunama?
Luka 11 in Litafi Mai-tsarki