Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 11:39-49 in Hausa

Help us?

Luka 11:39-49 in Litafi Mai-tsarki

39 Amma sai Ubangiji ya ce da shi, “Ku Farisawa kuna tsabtace bayan kofi da bangaji, amma cikin yana cike da kazamta da mugunta.
40 Ku mutane marasa tunani, wanda ya yi wajen, ba shine ya yi cikin ba?
41 Ku bayar da abin da ke ciki ga matalauta, kuma dukan abu zai zamar maku da tsafta.
42 Amma kaitonku Farisawa, gama kuna karbar zakka da daddoya da karkashi da kowanne irin ganye na lambu, amma kun watsar da adalci da kaunar Allah. Dole ne a yi adalci, a kaunaci Allah, a yi sauran abubuwan kuma.
43 Kaitonku Farisawa, domin kuna so a ba ku wuraren zama masu kyau a cikin masujadai, a kuma yi maku gaisuwar bangirma a cikin kasuwanni.
44 Kaiton ku, gama kuna kama da kabarbarun da ba yi masu shaida ba, mutane kuwa suna tafiya akansu ba tare da saninsu ba.”
45 Wani malami a cikin shari'ar Yahudawa ya amsa masa ya ce, “Malam, abin da ka ce ya bata mana rai mu ma.”
46 Sai Yesu ya ce, “Kaitonku malaman shari'a! Gama kun dora wa mutane kaya mai nauyi wanda ya fi karfinsu dauka. Amma ku, ko da dan yatsa ba ku taba kayan ba.
47 Kaiton ku, gama kuna gina abubuwan tunawa a kabuburan annabawa, alhali kuwa kakanni-kakanninku ne suka kashe su.
48 Ya zama kenan kuna sane da ayyukan kakanni-kakanninku, domin sune suka kashe annabawan da kuke tunawa da su.
49 Saboda wannan daliline hikimar Allah ta ce, “Zan aika manzanni da annabawa a wurinsu, kuma za su tsananta masu har ma za su kashe wadansu daga cikinsu.'
Luka 11 in Litafi Mai-tsarki