Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 11:27-29 in Hausa

Help us?

Luka 11:27-29 in Litafi Mai-tsarki

27 Ya zama, lokacin da ya ke fadin wadannan abubuwa, wata mace ta tada muryarta a cikin taron mutanen ta ce da shi, “Mai albarka ne cikin da ya haife ka, da maman da ka sha.”
28 Sai shi kuma ya ce, “Masu albarka ne wadanda suke jin maganar Allah suke yin biyayya da ita.”
29 Lokacin da mutane suke kara taruwa, sai ya fara cewa, “Wannan tsara, muguwar tsara ce. Ta na neman alama, Ko da yake ba wata alamar da za a bata sai irin ta Yunusa.
Luka 11 in Litafi Mai-tsarki