Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 9:5-13 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 9:5-13 in Litafi Mai-tsarki

5 Shawulu ya amsa, “Wanene kai, Ubangiji?” Ubangiji ya ce, “Nine Yesu wanda kake tsanantawa;
6 amma ka tashi, ka shiga cikin birnin, kuma za a gaya maka abinda lallai ne kayi.
7 Mutanen da ke tafiya tare da Shawulu suka tsaya shiru sun rasa abin fada, suna sauraron muryar, amma ba su ga kowa ba.
8 Shawulu ya tashi daga kasa, kuma daga ya bude idanunsa, baya ganin komai; sai suka kama hannuwansa suka yi masa jagora suka kawo shi cikin birnin Dimashku.
9 Har kwana uku ba ya kallo, kuma ba ya ci balle sha.
10 Akwai wani almajiri a Dimashku mai suna Hananiya; sai Ubangiji ya yi magana da shi cikin wahayi, ya ce, “Hananiya.” Sai ya ce, “Duba, gani nan Ubangiji.”
11 Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi titin da ake kira Mikakke, kuma a gidan wani mai suna Yahuza ka tambaya mutum daga Tarsus mai suna Shawulu; gama yana addu'a;
12 kuma ya gani cikin wahayi mutum mai suna Hananiya na shigowa kuma ya daura masa hannu, domin idanunsa su bude.”
13 Amma Hananiya ya amsa, “Ubangiji, na ji labari daga wurin mutane da yawa game da mutumin nan, da irin muguntar da ya aikata ga tsarkakan mutanenka da ke Urushalima.
Ayyukan Manzanni 9 in Litafi Mai-tsarki