Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 9:27-30 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 9:27-30 in Litafi Mai-tsarki

27 Amma Barnaba ya dauke shi ya kawo shi wurin manzannin. Ya kuwa gaya musu yadda Shawulu ya sadu da Ubangiji a hanya, har Ubangiji ya yi magana da shi, kuma yadda Shawulu ya yi wa'azi cikin sunan Yesu gabagadi a Dimashku.
28 Ya sadu da su lokacin shigar su da fitar su a Urushalima. Ya yi wa'azi gabagadi cikin sunan Ubangiji Yesu
29 kuma yana muhawara da Yahudawan Helenanci; amma sun ci gaba da kokarin kashe shi.
30 Da 'yan'uwa suka gane haka, sai suka kawo shi Kaisariya, suka kuwa tura shi zuwa Tarsus.
Ayyukan Manzanni 9 in Litafi Mai-tsarki