Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 8:16-27 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 8:16-27 in Litafi Mai-tsarki

16 Domin har wannan lokaci, Ruhu Mai Tsarki bai sauko kan kowannensu ba; an dai yi masu baftisma ne kadai cikin sunan Ubangiji Yesu.
17 Sai Bitrus da Yahaya suka dora masu hannuwansu, sai suka karbi Ruhu Mai Tsarki.
18 Sa'adda Siman yaga ana bayar da Ruhu Mai Tsarki ta wurin dorawar hannuwan manzanni, ya basu kudi.
19 Ya ce, “Ku bani wannan iko, ni ma, don duk wanda na dora wa hannu ya karbi Ruhu Mai Tsarki.”
20 Amma Bitrus yace masa, “Azurfarka ta lalace tare da kai, saboda kana tunanin za ka malaki baiwar Ubangiji da kudi.
21 Baka da wani rabo a wannan al'amari, domin zuciyarka ba daidai take da Allah ba.
22 Saboda haka ka tuba daga wannan muguntarka, ka kuma yi addu'a ga Ubangiji, domin mai yiwuwa ya gafarta maka game da manufar zuciyarka.
23 Domin na gane kana cikin bacin rai da kuma cikin daurin zunubi.”
24 Siman ya amsa ya ce, “Kayi addu'a ga Ubangiji domina, kada wani daga cikin abubuwan nan da ka fada ya faru da ni.”
25 Sa'anda Bitrus da Yahaya suka bada shaida kuma suka fadi maganar Ubangiji, sun koma Urushalima; akan hanya, suka yi wa'azin bishara a kauyukan samariyawa da yawa.
26 Yanzu kuwa Mala'ikan Ubangiji ya yi wa Filibus magana cewa, “Tashi ka tafi ta kudu da hanyar da ta yi kasa daga Urushalima zuwa Gaza” (wannan hanyar yana cikin hamada.)
27 Ya kuwa tashi ya tafi. Sai ga wani mutum daga Habasha, baba ne mai babban matsayi a karkashin Kandakatu, sarauniyar Habasha. Shine yake mulkin dukan dukiyarta. Ya zo Urushalima domin ya yi ibada.
Ayyukan Manzanni 8 in Litafi Mai-tsarki