Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 5:25-34 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 5:25-34 in Litafi Mai-tsarki

25 Sai wani ya zo ya ce masu, “Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a.”
26 Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu.
27 Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su,
28 cewa “Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu.”
29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba.
30 Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace,
31 Allah kuwa ya daukaka shi a hannun damarsa, domin ya zama sarki da kuma mai ceto, ya ba Isra'ila tuba da gafarar zunubai.
32 Mu kuwa shaidu ne ga wadannan al'amura, haka ma Ruhu Mai Tarki, wanda Allah ya bayar ga dukan wadanda suka yi biyayya a gareshi.”
33 Da yan majalisa suka ji haka sai suka fusata kwarai da gaske, har suka nemi su kashe manzannin.
34 Amma wani Bafarise mai suna Gamaliel, malami ne kuma na attaura wanda dukan jama'a suna martabawa, sai ya mike ya ba da umarni cewa a fid da manzannin waje na dan lokaci.
Ayyukan Manzanni 5 in Litafi Mai-tsarki