Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 5:15-24 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 5:15-24 in Litafi Mai-tsarki

15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu.
16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka.
17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka
18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku.
19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce,
20 “Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai.”
21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin.
22 Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto,
23 Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba.
24 Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar.
Ayyukan Manzanni 5 in Litafi Mai-tsarki