Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 5:11-30 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 5:11-30 in Litafi Mai-tsarki

11 Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura.
12 Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu,
13 Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a.
14 Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata,
15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu.
16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka.
17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka
18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku.
19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce,
20 “Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai.”
21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin.
22 Amma ma'aikatan da suka je kurkukun basu sami kowa, a kurkukunba, sai suka dawo suka ba da rahoto,
23 Su ka ce kurkukun a rufe gam da masu gadi suna nan a tsaye a bakin kofar amma da muka shiga, bamu sami kowa a ciki ba.
24 Yanzu sa'adda shugaban haikalin da manyan firistoci suka ji wadannan kalamai, sai suka rikice sosai game da su, suka ce yanzu me wannan zai haifar.
25 Sai wani ya zo ya ce masu, “Wadannan mutanen da kuka jefa a kurkuku suna can a cikin haikali suna koyar da jama'a.”
26 Sai shugaban haikalin ya je da ma'aikatansa suka kawosu, ba tare da tashin hankali ba, domin gudun kada jama'a su jejjefesu.
27 Da suka kawo su, sai suka gabatar da su gaban majalisa, babban firist kuwa ya tuhume su,
28 cewa “Ba mun yi maku kashedi da karfi kada ku yi koyarwa cikin wannan sunan ba? Amma ga shi duk kun cika Urushalima da koyarwarku, kuna kuma neman kusa jinin mutumin nan ya sauko kanmu.”
29 Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Dole mu yi wa Allah biyayya ba mutane ba.
30 Allah na ubanenmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe, ta wurin rateye shi a bisa itace,
Ayyukan Manzanni 5 in Litafi Mai-tsarki