Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 5:1-21 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 5:1-21 in Litafi Mai-tsarki

1 Sai wani mai suna Hananiya da matarsa Safiratu, suka sayar da filinsu,
2 Hananiya kuwa ya boye wasu daga cikin kudin filin, (kuma da sanin matarsa), sa'annan suka kawo ragowar kudin a gaban manzannin.
3 Amma Bitrus ya ce, “Hananiya don me shaidan ya cika zuciyarka, har ka yi wa Ruhu Mai Tsarki karya? Har ka boye wasu daga kudin filin?
4 Sa'adda ba ka sayar da filin ba, ba mallakarka bane? Bayan da ka sayar ma, ba naka bane? Don me kayi irin wannan tunanin a zuciyarka? To ba mutane ka yi wa karya ba, Allah ka yi wa.”
5 Nan take da jin haka, Hananiya ya fadi ya ja numfashinsa na karshe. Dukan mutanen da suka ji labarin kuwa tsoro mai girma ya afko masu
6 Matasa suka zo suka nannade gawarsa, suka fitar da shi waje suka binne shi.
7 Bayan wajen sa'a uku, sai matarsa ta iso, ba tare da sanin abin da ya faru ba.
8 Sai Bitrus ya ce mata, “ki gaya mini ko nawa kuka sayar da filin?” Sai ta amsa, “ta ce kaza ne.”
9 Sa'annan Bitrus ya ce mata, “Don me kuka shirya wannan makidar tare da mijinki don ku gwada Ruhun Ubangiji? Kiji tafiyar wadanda suka bizne mijinki a bakin kofa, kuma za su dauke ki yanzu.”
10 Nan take sai ta fadi a gabansa, ta ja numfashinta na karshe, matasan kuwa suka zo suka same ta ta mutu; sai suka dauki gawarta suka kai waje suka kuma bizne ta kusa da mijinta.
11 Tsoro mai girma kuwa ya afko wa iklisiyar gaba daya da dakan wadanda suka ji wadan nan al'amura.
12 Ayyukan alamu da ban mamaki masu yawa kuwa sun faru ga mutane, ta hannun manzannin. Dukansu kuma suna nan tare a dakalin Sulaimanu,
13 Sai dai babu mai karfin halin ya hada kai tare dasu; amma suna da kwarjini sosai a gaban jama'a.
14 Har wa yau aka rika samun karin masu ba da gaskiya, dinbin jama'a, maza da mata,
15 har sukan dauki marasa lafiya su kai su bakin titi, suna kwantar da su a bisa gadaje da shinfidu, domin idan Bitrus ya zo wucewa ko da inuwarsa ma ta taba wasunsu.
16 Mutane dayawa kuwa sukan zo daga garuruwan da ke kewaye da Urushalima, suna kuma kawo masu rashin lafiya, da wadanda aljannu ke damunsu, aka kuma warkar da su duka.
17 Amma babban firist ya taso tare da duk wadanda ke tare da shi (wato 'yan darikar Sadukiyawa); suka cika da kishi matuka
18 suka kama manzannin suka kuma jefasu a kurkuku.
19 A cikin dare sai mala'ikan Ubangiji ya bude kofofin kurkukun ya kuma fito da su waje, ya ce,
20 “Kuje ku tsaya a gaban haikali ku kuma gaya wa mutane maganar wannan rai.”
21 Sa'adda suka ji haka, sai suka tafi haikalin da wayewar gari suka yi koyarwa. Amma babban firist da jama'arsa suka zo suka kuma kira taro da kuma dukan yan majalisa, da dattawan jama'ar Isra'ilawa suka fito suka kuma ba da umarni, a fito masu da manzannin.
Ayyukan Manzanni 5 in Litafi Mai-tsarki