Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 4:33-37 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 4:33-37 in Litafi Mai-tsarki

33 Da iko mai karfi manzannin suka yi shelar shaidarsu game da tashin Yesu Ubangiji daga matattu, babban alheri kuma na bisansu.
34 Babu wani a cikinsu wanda ya rasa komai, domin masu filaye da gidaje suka sayar suka kawo kudin abin da suka sayar
35 sai suka kawo kudin gaban manzanni. Aka rarraba wa kowanne mutum bisa ga bukatarsa.
36 Yusufu, Balawi, mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannisu ka yi wa lakani da suna Barnaba. (wato, mai karfafa zuciya).
37 Yana da fili sai ya sayar da shi ya kawo kudin gaban manzanni.
Ayyukan Manzanni 4 in Litafi Mai-tsarki