Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 3:23-26 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 3:23-26 in Litafi Mai-tsarki

23 Zai kasance kowanne mutum da bai saurari annabin nan ba za a kau da shi gabadaya daga cikin mutanensa.'
24 I, dukan annabawa tun daga Sama'ila da wadanda suka zo bayansa, sun yi magana sun ambaci wadannan kwanaki.
25 Kune 'ya'yan annabawa da na alkawari wanda Allah ya yi da kakanninku, yadda ya ce wa Ibrahim, 'Daga zuriyarka dukan al'uman duniya za su sami albarka.'
26 Bayan da Allah ya ta da bawansa, a gareku ne ya fara aiko shi, domin ya albarkace ku tawurin juyadda kowannenku daga muguntarsa.”
Ayyukan Manzanni 3 in Litafi Mai-tsarki