Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 2:40-45 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 2:40-45 in Litafi Mai-tsarki

40 Da maganganu da yawa ya ba da shaida kuma ya karfafa su; ya ce, “Ku ceci kan ku daga wannan muguwar tsara.”
41 Sai suka karbi maganar sa kuma aka yi ma su baftisma, a wannan rana kuma aka sami karin rayuka wajen dubu uku.
42 Su ka cigaba cikin koyarwar manzanni da zumunta, cikin kakkaryawar gurasa da kuma cikin addu'o'i.
43 Tsoro ya sauko bisa kowane rai, kuma aka yi abubuwan ban mamaki da alamu da yawa ta wurin manzannin.
44 Duka wadanda suka ba da gaskiya suna tare kuma komai nasu na kowanensu ne,
45 kuma suka saida kadarorinsu da mallakarsu kuma suka rarrabawa kowa, bisa ga irin bukatar da kowannensu yake da ita.
Ayyukan Manzanni 2 in Litafi Mai-tsarki