Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 27:2-10 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 27:2-10 in Litafi Mai-tsarki

2 Muka shiga Jirgin ruwa daga Adramatiya, wanda ke shirin tashi zuwa kusa da gefen tekun Asiya. Sai muka je teku. Aristakus mutumin Tasalonika a Makidoniya ya tafi tare damu.
3 Washegari muka sauka birnin Sidon, inda Yuliyas ya nuna wa Bulus karamci ya kuma yarda abokansa su bi shi don ya kula da su.
4 Daga wurin, muka bi teku muka tafi ta Tsibirin Kubrus, domin matsananciyar iska da ke gaba damu.
5 Sa'adda muka ketare ruwa zuwa sassan Kilikiya da Bamfiliya, muka zo Mira ta birnin Lisiya.
6 Anan, jarumin ya sami jirgin ruwa daga Iskandariya wanda za shi Italiya. Ya samu cikinsa.
7 Kwana da kwanaki muna tafiya a hankali a karshe da kyar muka sauka kusa da Sinidus, iska ta hana mu tafiya, sai muka ratsa ta Karita, kusa da Salmina.
8 Da wahala muka bi ta makurda har muka zo wani wuri da ake kira Mafaka Mai Kyau wanda ke kusa da birnin Lasiya.
9 Yanzu mun dauki dogon lokaci, gashi lokacin azumin Yahudawa ya wuce, tafiyar kuma ta zama da hatsari. Bulus ya gargade su,
10 ya ce, “Jama'a, na gane tafiyarmu zata zamar mana da barna da asara mai yawa, ba ga kaya da jirgin kadai ba amma har da rayukan mu.”
Ayyukan Manzanni 27 in Litafi Mai-tsarki