Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 26:15-32 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 26:15-32 in Litafi Mai-tsarki

15 Sai na ce, 'Wanene kai ya Ubangiji?' Ubangiji ya amsa, 'Ni ne Yesu wanda kake tsanantawa.
16 Yanzu ka tashi tsaye domin saboda wannan dalili ne na bayyana gare ka in sanya ka, ka zama bawa da mashaidi na game da abubuwan da ka sani a kaina yanzu da wadanda zan bayyana maka daga bisani;
17 Zan kubutar da kai daga wurin mutane da kuma al'ummai da zan aike ka wurinsu,
18 domin ka bude idanunsu ka juyo su daga duhu zuwa haske da daga ikon Shaidan zuwa ga Allah, domin su karbi gafarar zunubai da gado da zan ba wadanda na kebe wa kaina ta wurin bangaskiya gare ni.'
19 Saboda haka, sarki Agaribas, ban yi rashin biyayya da wahayin da na gani daga sama ba;
20 amma, da farko ga wadanda ke a Dimashku, sa'annan a Urushalima da kasar Yahudiya gaba daya, da dukan Al'ummai, na yi wa'azi domin su tuba su kuma juyo ga Allah, su yi ayyukan da suka chanchanci tuba.
21 Domin wannan dalili ne Yahudawa suka kama ni a cikin haikali kuma suke kokari su kashe ni.
22 Allah ya taimake ni har wa yau, domin in iya tsayawa gaban mutane kanana da manya, in bada shaida game da iyakar abin da annabawa da Musa suka fada zai faru;
23 wato lallai Almasihu zai sha wahala, ya kuma zama na farko da za'a rayar daga matattu ya kuma yi shelar haske zuwa ga mutanen Yahudawa da Al'ummai.”
24 Da Bulus ya gama kare kansa, Festas ya yi magana da babban murya, “Bulus, kana hauka; yawan iliminka yasa ka hauka.”
25 Amma Bulus ya ce, “Ba na hauka, ya mai girma Festas; amma da karfin zuciya nake fadi kalmomin gaskiya da na natsuwa.
26 Saboda sarkin ya san wadannan abubuwa duka; shi ya sa nake magana gabagadi, don na hakikance cewa, ba abin da ke a boye gare shi; gama ba a yi wadannan abubuwa a boye ba.
27 Ko ka gaskanta da annabawa, Sarki Agaribas? Na sani ka gaskanta.”
28 Agaribas ya ce wa Bulus, “A cikin karamin lokaci kana so ka rinjaye ni ka mai da ni Krista?”
29 Bulus ya ce, “Ina roko ga Allah, domin ko a karamin lokaci ko a dogon lokaci, ba kai kadai ba, amma har da wadanda ke sauraro na yau su zama kamar ni, amma ban da wadannan sarkokin.”
30 Sai sarki ya tashi tsaye tare da gwamna da Barniki da dukan wadanda ke zaune tare da su;
31 da suka bar dakin taron, suka ci gaba da magana da juna suna cewa, “Wannan mutum bai yi wani abin da ya chanchanci mutuwa ko kuma dauri ba.”
32 Agaribas ya ce wa Fastos, “Da mutumin nan bai daukaka kara zuwa ga Kaisar ba da an sake shi.”
Ayyukan Manzanni 26 in Litafi Mai-tsarki