Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 24:5-20 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 24:5-20 in Litafi Mai-tsarki

5 An iske mutumin nan yana barna irir iri, yana kuma zuga jama'ar Yahudawa a dukan duniya su yi tayarwa.
6 Har ma ya yi kokarin kazantar da haikali; saboda haka muka kama shi. Mun so mu shari'anta masa bisa ga dokarmu.
7 Amma Lisiyas jami'i ya zo ya kwace shi da karfi daga hannunmu.
8 Idan ka binciki Bulus game da wadannan al'amura, kai ma, zai tabbatar maka abin da muke zarginsa a kai.
9 Dukan Yahudawa suna zargin Bulus cewa wadannan abubuwa gaskiya ne.
10 lokacin da gwamnan ya alamta wa Bulus ya yi magana sai yace, “Yanzu na fahimci cewar da dadewa kana mulkin kasarnan, don haka da farin ciki zan yi maka bayani.
11 Zaka iya tabbatarwa cewa bai kai kwana sha biyu ba tun da nake zuwa Urushalima don yin sujada.
12 Da suka same ni a haikali, ban yi jayayya ko kawo rudami a tsakanin jama'a ba.
13 Don haka ba su da tabbas akan abinda suke zargina a kansa yau.
14 Amma na sanar da kai, bisa ga abin da suke kira darika, haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu. Na yi aminci wajen kiyaye dukan abin da ke a rubuce a Attaurat da litattafan annabawa.
15 Ina sa bege ga Allah, kamar yadda za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu;
16 a kan haka kuma, nake kokarin zama mara abin zargi a gaban Allah da mutane ina yin haka cikin dukan al'amura.
17 Bayan wadansu shekaru na zo in kawo wasu sadakoki da baikon yardar rai.
18 Cikin kudurin yin haka, sai wasu Yahudawa daga kasar Asiya suka iske ni a cikin ka'idodin tsarkakewa a haikali, ba da taro ko ta da hargitsi ba.
19 Yakamata wadannan mutanen su zo gabarka a yau, har idan suna da wani zargi a kai na.
20 In kuwa ba haka ba bari mutanennan su fada in sun taba iske ni da wani aibu a duk lokacin da na gurfana a gaban majalisar Yahudawa;
Ayyukan Manzanni 24 in Litafi Mai-tsarki