Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 21:14-33 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 21:14-33 in Litafi Mai-tsarki

14 Tun da Bulus bashi da niyyar a rinjaye shi, muka daina kuka muka ce, “Bari nufin Ubangiji ya tabbata.”
15 Bayan wadannan kwanaki, muka dauki jakkunanmu muka haura Urushalima.
16 Wadansu almjirai daga Kaisariya suka bi mu. Sun zo ne tare da wani ana ce da shi Manason, mutumin Kuburus mai bi na farko, wanda za mu zauna da shi.
17 Da muka isa Urushalima, 'yan'uwa suka marabce mu da farin ciki.
18 Washegari Bulus ya tafi tare da mu zuwa wurin Bitrus, dukan dattawa kuma suna nan.
19 Bayan ya gaishe su, sai ya shaida masu daya bayan daya abubuwan da Allah ya yi cikin al'ummai ta wurin hidimarsa.
20 Da suka ji haka, suka yabi Ubangiji suka ce masa, “Ka gani, dan'uwa, dubban Yahudawa sun bada gaskiya suna kuma da niyyar kiyaye shari'a.
21 An kuma gaya masu a kanka cewa, kana koya wa Yahudawan da suke zaune cikin al'ummai su yi watsi da Musa. Kana koya masu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, kada kuma su bi tsofaffin al'adu.
22 Me ya kamata mu yi? Hakika za su ji ka zo.
23 Sabo da haka ka yi abin da muka fada maka yanzu. Muna da maza hudu da suka dauki wa'adi.
24 Tafi da wadannan ka tsarkake kanka tare da su, ka dauki dukan dawainiyar su dana askin kai. Ta haka kowanne mutum zai sani abubuwan da ake fadi a kanka karya ne. Za su sani cewa kai mai kiyaye shari'a ne.
25 Game da al'umman da suka bada gaskiya mun yi masu wasika, mun bada umarni su kaurace kansu daga sadakokin da aka mika wa gumaku, da jini, da abin da aka makare da kuma fasikanci.
26 Sai Bulus ya dauki mazannan, washegari ya tsarkake kansa tare da su, suka shiga haikali, domin ya sanar da cikar ranakun tsarkakewarsu, wato ranar ba da sadaka domin kowanne dayansu.
27 Da kwanakin nan bakwai suka yi gab da cika, wadansu Yahudawa daga Asiya suka ga Bulus a haikali, sai suka zuga taro, suka danke shi.
28 Suna ta kururuwa, “Mutanen Isra'ila ku taimaka mana. Wannan shine mutumin da ke koya wa dukan mutane ko'ina abubuwa gaba da mutane, da shari'a da kuma wannan wurin. Banda haka ya kawo Helenawa cikin haikalin nan ya kazantar da wannan wuri tsatsarka.”
29 Domin dama sun ga Tarofimas mutumin Afisa tare da Bulus cikin birni, suka yi zaton ya kawo shi cikin haikali.
30 Sai duk gari ya rude, mutane suka runtuma suka danke Bulus. Suka ja shi waje daga cikin haikalin, nan da nan aka rufe kofofin.
31 Suna kokarin kashe shi kenan, sai labari ya kai wurin hafsan sojoji cewa Urushalima duk ta yamutse da tarzoma.
32 Nan take ya dauki mayaka da jarumawa, suka sheka da gudu wurin taron. Da mutane suka ga hafsan sojoji da rundunansa sai suka daina dukan Bulus.
33 Sai hafsan ya tafi ya danke Bulus ya sa aka daure shi da sarkoki biyu. Ya tambaya ko shi wanene da kuma laifinsa.
Ayyukan Manzanni 21 in Litafi Mai-tsarki