Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 1:3-19 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 1:3-19 in Litafi Mai-tsarki

3 Bayan ya sha wahala, ya bayyana kan sa da rai a garesu, da alamu da dama masu gamsarwa. Kwana arba'in ya baiyana kansa a garesu yana yi masu magana game da mulkin Allah.
4 Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, “Kun ji daga gare ni,
5 cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan.”
6 Sa'adda suna tare suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci ne za ka maido da mulki ga Isra'ila?”
7 Ya ce masu, “Ba naku bane ku san lokaci ko sa'a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa.
8 Amma za ku karbi iko, idan Ruhu Mai Tsarki ya zo bisanku, sa'annan za ku zama shaidu na cikin Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, har ya zuwa karshen duniya.”
9 Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu.
10 Da suka dinga kallon sama yayin da ya tafi, nan da nan, mazaje biyu suka tsaya a gabansu cikin fararen tufafi.
11 Suka ce, “Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama.”
12 Da suka dawo Urushalima daga dutsen Zaitun, wanda ke kusa da Urushalima, tafiyar Asabaci daya ne.
13 Da suka iso, sai suka haye zuwa cikin bene inda suke da zama. Sune su Bitrus, Yahaya, Yakubu, Andarawus, Filibus, Toma, Bartalamawus, Matiyu, Yakubu dan Alfa, Siman mai tsattsauran ra'ayi, kuma da Yahuza dan Yakubu.
14 Dukansu kuwa suka hada kai gaba daya, yayin da suka ci gaba da naciya cikin addu'a. Tare da su kuma akwai mata, Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.
15 A cikin wadannan kwanaki Bitrus ya tashi tsaye a tsakiyar 'yan'uwa, kimanin mutane dari da ashirin, ya ce,
16 “'Yan'uwa, akwai bukatar Nassi ya cika, wanda Ruhu Mai Tsarki ya fada a baya ta bakin Dauda game da Yahuza, wanda ya jagoranci wadanda suka kama Yesu
17 Domin yana daya daga cikinmu kuma ya karbi rabonsa na ladan wannan hidima,”
18 (Wannan mutum fa ya sai wa kansa fili da cinikin da ya yi na muguntarsa, kuma a nan ya fado da ka, cikinsa ya fashe, hanjinsa suka zubo waje.
19 Duka mazaunan Urushalima suka ji wannan, saboda haka suka kira wannan fili da harshensu “Akeldama” wato, “Filin Jini.”)
Ayyukan Manzanni 1 in Litafi Mai-tsarki