Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 1

Ayyukan Manzanni 1:20-26

Help us?
Click on verse(s) to share them!
20“Domin an rubuta a littafin Zabura, 'Bari filinsa ya zama kufai, kada a bar kowa ya zauna wurin,' kuma, 'Bari wani ya dauki matsayinsa na shugabanci.'
21Saboda haka ya zama dole, daya daga cikin wadanda suke tare da mu tun lokacin da Ubangiji Yesu yana shiga da fita, a tsakaninmu,
22farawa daga baftismar yahaya har zuwa ranar da aka dauke shi daga wurinmu zuwa sama, ya zama daya daga cikin mu wurin shaidar tashinsa.”
23Suka gabatar da mutum biyu, Yusufu wanda ake kira Barsabbas, wanda kuma aka yiwa suna Justus, da kuma Matayas.
24Su ka yi addu'a suka ce, “Ubangiji, kai ka san zuciyar dukan mutane, ka bayyana mana wanda ka zaba cikin su biyun nan
25Domin ya dauki gurbin da kuma manzancin daga inda Yahuza ya kauce zuwa nashi waje”
26suka jefa kuri'a a kansu; zabe ya fada kan Matayas kuma suka lissafta shi tare da manzanni sha dayan.

Read Ayyukan Manzanni 1Ayyukan Manzanni 1
Compare Ayyukan Manzanni 1:20-26Ayyukan Manzanni 1:20-26