19 Duka mazaunan Urushalima suka ji wannan, saboda haka suka kira wannan fili da harshensu “Akeldama” wato, “Filin Jini.”)
20 “Domin an rubuta a littafin Zabura, 'Bari filinsa ya zama kufai, kada a bar kowa ya zauna wurin,' kuma, 'Bari wani ya dauki matsayinsa na shugabanci.'
21 Saboda haka ya zama dole, daya daga cikin wadanda suke tare da mu tun lokacin da Ubangiji Yesu yana shiga da fita, a tsakaninmu,
22 farawa daga baftismar yahaya har zuwa ranar da aka dauke shi daga wurinmu zuwa sama, ya zama daya daga cikin mu wurin shaidar tashinsa.”
23 Suka gabatar da mutum biyu, Yusufu wanda ake kira Barsabbas, wanda kuma aka yiwa suna Justus, da kuma Matayas.