Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 19:29-31 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 19:29-31 in Litafi Mai-tsarki

29 Gari gaba daya ya rude, jama'a kuma sun hanzarta zuwa wurin taron. Kafin wannan lokaci, sun riga sun kama abokan tafiyar Bulus, wato Gayus da Aristakas wadanda suka zo daga Makidoniya.
30 Bulus ya yi niyya ya shiga cikin taron jama'ar, amma almajiran suka hana shi.
31 Haka nan ma wadansu abokan Bulus da ke shugabanin yankin al'umma Asiya sun aika masa da roko mai karfi kada ya shiga dandalin.
Ayyukan Manzanni 19 in Litafi Mai-tsarki