Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 19:27-39 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 19:27-39 in Litafi Mai-tsarki

27 Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada.”
28 Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa “Mai girma ce Dayana ta Afisa.”
29 Gari gaba daya ya rude, jama'a kuma sun hanzarta zuwa wurin taron. Kafin wannan lokaci, sun riga sun kama abokan tafiyar Bulus, wato Gayus da Aristakas wadanda suka zo daga Makidoniya.
30 Bulus ya yi niyya ya shiga cikin taron jama'ar, amma almajiran suka hana shi.
31 Haka nan ma wadansu abokan Bulus da ke shugabanin yankin al'umma Asiya sun aika masa da roko mai karfi kada ya shiga dandalin.
32 Wadansu mutane na kirarin wani abu, wadansu kuma na kirarin wani abu dabam, domin jama'a sun rude. Da yawa daga cikinsu ma ba su san dalilin taruwarsu ba.
33 Yahudawa suka kawo Iskandari ya tsaya a gaban taruwan jama'a. Iskandari ya mika hannunsa sama domin ya yi bayani ga jama'a.
34 Amma da suka gane shi Bayahude ne, sai dukansu suka kwala ihu wajen sa'a biyu, “Mai girma ce Dayana ta Afisa.”
35 Da magatakardar garin ya sha kan jama'a, sai ya ce, “Ya ku mutanen Afisa, wanene bai san cewa birnin Afisa cibiya ce na allahn nan Dayana mai girma da na sifar da ta fado daga sama ba?
36 Tun da ba a karyata wadannan abubuwa ba, ya kamata ku yi shuru don kada ku yi wani abu a gaggauce.
37 Gama kun kawo wadannan mutane a wannan dakin sharia ba a kan su mafasa ne na haikali ba ko kuma masu sabo ga allahnmu ba.
38 Saboda haka idan Damatrayas da makeran da ke tare da su na da wata tuhuma a kan wani, kotuna suna nan a bude masu shari'a kuma suna nan. Ba ri su kai karar junansu.
39 Amma idan akwai maganganu na dubawa, za a daidaita su a taronmu na lokaci lokaci.
Ayyukan Manzanni 19 in Litafi Mai-tsarki