Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 17:2-12 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 17:2-12 in Litafi Mai-tsarki

2 Bulus, kamar yadda ya saba, ya nufi wurinsu, yana tattaunawa da su har Asabaci uku, daga cikin littattafai.
3 Bulus ya bude littattafai yana bayyana masu cewa, dole ne Almasihu ya sha wahala, ya kuma tashi daga matattu. Ya ce, “Wannan Yesu kuwa da nake sanar maku, shine Almasihu”.
4 Wasu Yahudawa sun yarda, sun bi Bulus da Sila, da wadansu Helenawa, da Shugabannin Mata da jama'a da yawa.
5 Yahudawan da basu ba da gaskiya ba suka cika da kishi, suka dauki wadansu 'yan ta'adda daga cikin kasuwa, suka tada tarzoma cikin birnin, mutane da yawa na bin su. Sun kai hari a gidan Yason, da niyyar fitar da Bulus da Sila a gaban jama'a.
6 Amma da ba su ga Bulus da Sila ba, suka ja Yason da wasu 'yan'uwa masu bi zuwa gaban mahukuntar birnin, suna cewa, “Wadannan ne fa masu ta da zaune tsaye, gashi sun zo mana.
7 Wadannan mutane da Yason ya marabta, sun saba wa dokokin Kaisar; Suna cewa akwai wani sarki mai suna - Yesu.”
8 Da taron jama'a, da mahukuntan birnin suka ji haka, sun damu.
9 Bayan da sun amshi kudi daga wurin Yason da sauran 'yan'uwan, sai suka sake su.
10 A wannan daren, 'yan'uwa masu bi suka fitar da Bulus da Sila, suka aike su garin Biriya. Da isar su can, su ka nufa majami'ar Yahudawa.
11 Mutanen Biriya daban suke da na Tasalunika, sun yarda da sakon Bulus da zuciya daya, suna kuma binciken littattafai kowace rana domin su tabbatar da sakon Bulus, ko gaskiya ne.
12 Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa.
Ayyukan Manzanni 17 in Litafi Mai-tsarki