Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 17:17-28 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 17:17-28 in Litafi Mai-tsarki

17 Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami'a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa.
18 Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, “Menene wannan sakaren ke cewa?” Wadansu kuma sun ce, “Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam,” domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu.
19 Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, “Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka?
20 Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su.”
21 (Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su).
22 Bulus ya tsaya a tsakiyar Tudun Arasa ya ce, “Ku mutanen Atiniya na lura masu kwazon addini ne ku.
23 Na lura da abubuwan sujadar ku yayin da nake zagawa, amma na ga wani bagadi da rubutu a kansa mai cewa, “Ga Allah wanda ba a sani ba.” Abin da kuke bauta wa cikin rashin sani, shi nake sanar maku.
24 Allahn da ya yi duniya da kome da ke cikinta, tun da ya ke shine Ubangijin sama da kasa, ba ya zama a haikalin da mutane suka gina da hannu.
25 Ba ya neman taimakon kowa, babu kuma wanda ya isa ya ba shi. Shine ke ba da rai, da numfashi da kowanne abu.
26 Daga mutum daya ya hallici dukan al'umman duniya, ya rarraba, ya kuma sanya kowa a inda ya shirya masa.
27 Domin su nemi Allah ko za su iya kaiwa zuwa gareshi su same shi, ga shi kuwa ba ya nesa da kowannenmu.
28 A cikinsa muke rayuwa, muna walwala, kamar yadda wani daga cikin masananku yace, 'Mu 'ya'yansa ne'.
Ayyukan Manzanni 17 in Litafi Mai-tsarki