Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 17:12-21 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 17:12-21 in Litafi Mai-tsarki

12 Saboda haka mutane da yawa cikin su sun ba da gaskiya, tare da wadansu sannanun mata Helenawa da maza da yawa.
13 Amma da Yahudawan Tasalunika suka ji cewa Bulus yana wa'azin kalmar Allah a Biriya, sun haura can, sun tada hankulan jama'a.
14 Nan da nan, masu bi na Biriya sun dauki Bulus sun aika shi zuwa teku, an bar Sila da Timoti a Biriya tukuna.
15 Wadanda sun fitar da Bulus, sun kai shi har zuwa birnin Atina. Bulus ya ba su sako, su fada wa Sila da Timoti suyi hanzari su same shi.
16 Sa'anda Bulus yana jiran zuwan Sila da Timoti a Atina, ya yi fushi a ransa, da ya ga birnin cike da gumakai.
17 Ya tattauna da Yahudawa a cikin majami'a tare da masu yin sujada ga Allah, da kuma wadanda yake samu a kowace rana, a kasuwa.
18 Amma wadan su Abikuriyawa da masana sun yi karo da shi. Wadansun su na cewa, “Menene wannan sakaren ke cewa?” Wadansu kuma sun ce, “Da alama mai wa'azi ne na wasu alloli dabam,” domin yana wa'azin Yesu da tashin sa daga matattu.
19 Suka dauki Bulus zuwa Tudun Arasa, suna cewa, “Ko za ka sanar mana da wannan sabuwar koyaswar taka?
20 Abubbuwan da kake fadi, baki ne a gare mu. Muna so mu san ma'anar su.”
21 (Atiniyawa da bakin da ke cikinsu, suna ba da lokacin su ga fadin sabobbin abubuwa da sauraron su).
Ayyukan Manzanni 17 in Litafi Mai-tsarki