Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 16:36-38 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 16:36-38 in Litafi Mai-tsarki

36 Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, “Ku tafi cikin salama”.
37 Amma Bulus ya ce masu, “Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu.
38 Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne.
Ayyukan Manzanni 16 in Litafi Mai-tsarki