Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 16:25-38 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 16:25-38 in Litafi Mai-tsarki

25 Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su.
26 Nan da nan sai ga wata girgizar kasa, wadda ta sa ginshikan kurkukun sun kadu, nan da nan kofofin kurkukun sun bude, 'yan sarka kuma, sarkokin su sun karkatse.
27 Mai tsaron kurkukun ya tashi daga barci ya ga kofofin kurkukun a bude, ya zaro takobi, zai kashe kan sa, a tunanin sa, 'yan sarkar sun gudu.
28 Amma Bulus ya ta da murya da karfi, ya ce, “kada kayi wa kanka barna, domin dukan mu muna nan”.
29 Mai tsaron kurkukun ya aika a kawo fitila, ya shiga ciki a gurguje da rawan jiki, ya fadi a gaban Bulus da Sila,
30 ya fitar da su waje ya ce, “Shugabanni, me ya kamata in yi domin in tsira?”
31 Sun ce masa, “ka ba da gaskiya ga Yesu Ubangiji, da kai da gidan ka, za ku sami tsira”.
32 Bulus da Sila suka fada masa maganar Ubangiji, tare da iyalinsa.
33 Shi mai tsaron kurkukun ya dauke su cikin daren, ya wanke raunukansu, an kuma yi masa Baftisma nan da nan tare da iyalinsa.
34 Ya kai Bulus da Sila gidansa, ya ba su abinci. Murna ta cika gidan mai tsaron kurkukun, domin iyalin sa duka sun ba da gaskiya ga Allah.
35 Da gari ya waye, alkalai sun ba da sako a saki Bulus da Sila.
36 Mai tsaron kurkukun kuwa ya sanar wa Bulus wannan magana ta alkalan, saboda haka ya ce wa Bulus, “Ku tafi cikin salama”.
37 Amma Bulus ya ce masu, “Sun yi mana duka a fili a gaban mutane mu da muke Romawa, ba a kashe mu ba, sun kuma sa mu a kurkuku; suna koran mu a asirce? Su zo da kansu su fitar da mu.
38 Masu tsaron kurkuku sun mayar da maganar Bulus ga alkalan, wanda ya sa sun firgita, da jin cewa Bulus da Sila Romawa ne.
Ayyukan Manzanni 16 in Litafi Mai-tsarki