Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 16:18-25 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 16:18-25 in Litafi Mai-tsarki

18 Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, “Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu”. Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take.
19 Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta.
20 Da suka kai su Kotu, suka ce, “Wadannan mutane Yahudawa ne, suna kawo tashin hankali a birninmu.
21 Suna koyar da abubuwa da ba su karbuwa a gare mu, balle mu aikata, a matsayinmu na Romawa.”
22 Sai jama'a gaba daya sun tayar wa Bulus da Sila; alkalan kuma sun yage rigunansu, sun ba da umarni a duki Bulus da Sila da bulala.
23 Bayan dukan, an jefa su Bulus a kurkuku, an ba mai tsaron kurkukun umurni ya kulle su da kyau, kada su gudu.
24 Shi kuma ya yi hakanan, ya sa masu sarkoki a kafafun su, kamar yadda aka umurce shi.
25 Da tsakar dare, Bulus da Sila suna yin adu'a, su na raira wakoki ga Allah, sauran 'yan sarkar su na jin su.
Ayyukan Manzanni 16 in Litafi Mai-tsarki