Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 16:16-19 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 16:16-19 in Litafi Mai-tsarki

16 A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai.
17 Tana bin Bulus, tare da mu, tana fadi da murya mai karfi cewa, “Wadannan mutanen, bayin Allah mafi daukaka ne, suna sanar maku hanyar ceto ne”.
18 Ta dauki kwanaki tana haka. Amma Bulus ya yi fushi da ita ainun, ya juya ya umarci ruhun, ya ce, “Na umarce ka, ka rabu da ita a cikin sunan Yesu Almasihu”. Ruhun ya yi biyayya ya rabu da ita nan take.
19 Da iyayengijinta suka ga cewa hanyar shigar kudinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila, suka ja su cikin kasuwa suka kai su gaban mahunkunta.
Ayyukan Manzanni 16 in Litafi Mai-tsarki