Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 16:14-16 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 16:14-16 in Litafi Mai-tsarki

14 Wata mace mai suna Lidiya, 'yar kasuwa ce a birnin Tiyatira, mai bautar Allah ce, ta saurare mu. Ubangiji ya bude zuciyarta, ta mai da hankali ga maganar da Bulus ke fadi.
15 Sa'anda da aka yi mata Baftisma tare da mutanen gidanta, ta ce da mu, “Idan kun dauke ni mai bautar Allah, ku zo gidana ku zauna.” Sai ta rinjaye mu.
16 A daidai wannan lokaci, muna tafiya wurin addu'a, wata yarinya mai ruhun duba ta hadu da mu. Iyayen gijinta na arziki da ita sosai.
Ayyukan Manzanni 16 in Litafi Mai-tsarki