Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 15:29-34 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 15:29-34 in Litafi Mai-tsarki

29 ku bar yi wa gumaka hadaya, ku bar cin mushe da shan kayan maye da zina da faskanci, in kun kiyaye wadannan abubuwa za ku zauna lafiya. Ku huta lafiya.”
30 Da aka sallame su, sai suka je Antakiya. Bayan sun tara jama'a sai suka ba su wasikar.
31 Bayan da suka karanta ta, sai suka yi murna sosai saboda karfafawa.
32 Yahuza da Sila, da shike su annabawa ne, suka karfafa 'yan'uwa da kalmomi masu yawa.
33 Bayan sun yi kwananki a wurin, sai aka sallame su zuwa wurin 'yan'uwa wadanda suka aiko su.
34 Amma ya gamshe Sila ya zauna a wurin.
Ayyukan Manzanni 15 in Litafi Mai-tsarki