Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 14:9-19 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 14:9-19 in Litafi Mai-tsarki

9 Wannan mutumin ya ji Bulus yana magana. Bulus ya kafa masa ido, ya gane mutumin na da bangaskiya da za a warkar da shi. Sai ya ce masa da murya mai karfi, “Tashi ka tsaya akan kafafunka”
10 Sai mutumin ya yi tsalle ya fara tafiya da kafafunsa, yana yawo.
11 Da jama'an garin sun ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryarsu suna cewa da Likoniyanci, “Ai alloli sun ziyarce mu daga sama, da kamanin mutane.”
12 Suna kiran Barnaba da sunan “Zafsa,” Bulus kuwa suka kira shi da sunan “Hamisa” domin shine yafi yin magana.
13 Sai firist din zafsa wanda dakin yin masa sujada na kofar birni; ya kawo bijimai biyu da furannin da aka saka su kamar gammo; shi da jama'arsa suna so su yi masa hadaya.
14 Amma da manzannin, wato Barnaba da Bulus, su ka ji labarin, suka yage rigunansu, suka hanzarta zuwa gun taron mutanen.
15 Suna ta cewa, “Kuji! Ku mutane don me kuke wannan abin? Mu fa mutane ne kamarku. Mun kawo maku labari mai dadi ne, da cewa, ku rabu da abubuwa marar amfani, ku koma ga Allah mai rai, wanda ya hallici sama da kasa da teku da dukan abubuwa da ke cikinsu.
16 A da dai ya bar mutane su yi abinda suka ga dama.
17 Duk da haka, bai bar kansa ba tare da shaida ba, don yana bada abubuwa masu kyau, yana ba ku ruwan sama, lokatai masu albarka, ya cika ranku da abinci da farin ciki.”
18 Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya.
19 Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu.
Ayyukan Manzanni 14 in Litafi Mai-tsarki