Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 13:21-35 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 13:21-35 in Litafi Mai-tsarki

21 Sai jama'a suka roka a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Saul dan Kish, mutumin kabilar Binyamin ya zama sarki har na tsawon shekara arba'in.
22 Allah kuwa ya cire shi daga kan kujerar sarauta, ya daga Dauda ya zama sarkinsu. A kan Dauda ne Allah ya ce, 'Na sami Dauda dan Yessi, mutumin da zuciyata ke so; zai yi duk abin da nake so'.
23 Daga zuriyar mutumin nan Allah ya fito da mai ceto, Yesu, kamar yadda aka alkawarta zai yi.
24 Wannan ya faru kafin Yesu ya zo, Yahaya ya yi shelar baftimar tuba ga jamma'ar Isra'ila.
25 Sa'adda Yahaya ya gama aikin sa, sai ya ce, 'Wanene ni a tsamanin ku? Ba nine shi ba. Amma ku saurara, akwai wani mai zuwa bayana wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba.'
26 Yan'uwa 'ya'ya daga zuriyar Ibrahim, da wadanda ke bautar Allah a cikinku, saboda mune aka turo sakon ceto.
27 Saboda wadanda ke zaune cikin Urushalima, da masu mulkinsu, ba su gane shi ba, kuma sun cika fadin annabawa da a ke karantawa kowace ranar Asabaci ta wurin kashe shi.
28 Duk da cewa ba su sami dalilin mutuwa a kansa ba, suka roki Bilatus ya kashe shi.
29 Bayan sun gama duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka sauke shi daga giciye suka sa shi a cikin kabari.
30 Amma Allah ya tashe shi daga matattu.
31 Mutanen da suka zo tare da shi daga Galili da Urushalima kuwa suka yi ta ganinsa har kwanaki da yawa. Wadanan mutane kuma sune shaidunsa ga jama'a a yanzu.
32 Mun kawo maku labari mai dadi game da alkawaran da aka yi wa kakkaninmu.
33 Ubangiji ya bar mana alkawaran. Don haka ya ta da Yesu daga matattu. Kamar yadda ya ke a littafin zabura ta biyu: “Kai da na ne yau na zama mahaifinka.”
34 Kuma dalilin tayar da shi daga matattu shine saboda kada jikinsa ya rube, ya yi magana kamar haka: “Zan baku albarkun Dauda masu tsarki tabatattu.”
35 Wannan shine dalilin da ya yi magana kuma a wata Zabura, 'Ba za ka bar Mai Tsarkinka ya rube ba.'
Ayyukan Manzanni 13 in Litafi Mai-tsarki