Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 12:9-15 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 12:9-15 in Litafi Mai-tsarki

9 Bitrus kuwa ya bi mala'ikan suka fita waje. Bai gane abin da mala'ikan ke yi zahiri ne ba. Yana zaton ko yana ganin wahayi ne.
10 Bayan da suka wuce masu tsaron fari da na biyu, sun kai kofar da aka yi da karfe wadda ta mike zuwa cikin gari; ta bude masu da kanta. Suka fita sun bi titin, kuma nan take kuma sai mala'ikan ya bar shi.
11 Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, “Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato.”
12 Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a.
13 Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar.
14 Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa.
15 Suka ce mata, “Kin haukace.” Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, “Mala'ikansa ne.”
Ayyukan Manzanni 12 in Litafi Mai-tsarki