Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 12:4-8 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 12:4-8 in Litafi Mai-tsarki

4 Bayan ya kama shi, sai ya tsare shi a kurkuku ya kuwa sa sojoji hudu su dinga tsaron sa; yana niyyar kawo shi gaban mutanen a bayan Idin katarewa.
5 To, Bitrus na tsare a kurkuku, amma 'yan'uwa na iklisiya suna yin addu'a ga Allah sosai domin sa.
6 Ana kamar gobe Hiridus zai fitar da shi, a wannan daren, Bitrus yana barci a tsakanin sojoji biyu, daure da sarkoki biyu; sojoji kuma na gadi a bakin kurkukun.
7 Ba zato, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gareshi, haske ya haskaka dakin. Ya taba Bitrus a gefe ya tashe shi kuma ya ce, “Tashi da sauri.” Sai ga sarkokin suka zube daga hannunsa.
8 Mala'ikan ya ce masa, “Yi damara ka sa takalmanka.” Bitrus kuwa yayi haka. Mala'ikan ce ma sa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.”
Ayyukan Manzanni 12 in Litafi Mai-tsarki