Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 12:16-23 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 12:16-23 in Litafi Mai-tsarki

16 Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai.
17 Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, “Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru.” Sai ya bar su, ya tafi wani wuri.
18 Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus.
19 Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can.
20 Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne.
21 A ranan da aka kayyade, Hirudus ya sha damara da kayan saurata kuma ya zauna akan kursiyi; ya yi masu jawabi.
22 Mutanen suka yi ihu, “Wannan muryar allahce, ba ta mutum ba!”
23 Nan take mala'ika Ubangiji ya buge shi don bai ba Allah daukaka ba, nan take tsutsotsi suka cinye shi har ya mutu.
Ayyukan Manzanni 12 in Litafi Mai-tsarki