Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 12:11-20 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 12:11-20 in Litafi Mai-tsarki

11 Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, “Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato.”
12 Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a.
13 Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar.
14 Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa.
15 Suka ce mata, “Kin haukace.” Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, “Mala'ikansa ne.”
16 Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai.
17 Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, “Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru.” Sai ya bar su, ya tafi wani wuri.
18 Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus.
19 Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can.
20 Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne.
Ayyukan Manzanni 12 in Litafi Mai-tsarki