Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 11:9-20 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 11:9-20 in Litafi Mai-tsarki

9 Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, “Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki.”
10 Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama.
11 Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
12 Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
13 Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa “Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus.
14 Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka.”
15 Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko.
16 Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce, “Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki.”
17 To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah?
18 Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce “Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai.”
19 Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai.
20 Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu.
Ayyukan Manzanni 11 in Litafi Mai-tsarki