Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 11:7-12 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 11:7-12 in Litafi Mai-tsarki

7 Sai na ji murya tana ce da ni, “Tashi, Bitrus, yanka ka ci.”
8 Na ce, “Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina.”
9 Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, “Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki.”
10 Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama.
11 Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
12 Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
Ayyukan Manzanni 11 in Litafi Mai-tsarki