Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 11:24-28 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 11:24-28 in Litafi Mai-tsarki

24 Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji.
25 Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu.
26 Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista.
27 A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya.
28 Daya daga cikinsu, mai suna Agabas ya mike tsaye yayi magana da ikon Ruhu cewa za a yi tsanani fari ko'ina a duniya. Wannan ya faru ne a zamanin Kalaudiya.
Ayyukan Manzanni 11 in Litafi Mai-tsarki