Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 11:22-27 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 11:22-27 in Litafi Mai-tsarki

22 Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya.
23 Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su.
24 Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji.
25 Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu.
26 Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista.
27 A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya.
Ayyukan Manzanni 11 in Litafi Mai-tsarki