Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 11:15-23 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 11:15-23 in Litafi Mai-tsarki

15 Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko.
16 Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce, “Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki.”
17 To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah?
18 Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce “Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai.”
19 Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai.
20 Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu.
21 Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji.
22 Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya.
23 Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su.
Ayyukan Manzanni 11 in Litafi Mai-tsarki