5 “Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus.
6 Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku.
7 Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima.
8 Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa.
9 Washe gari wajen sa'a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu'a.