Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 10:32-42 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 10:32-42 in Litafi Mai-tsarki

32 Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku.
33 Idan ya zo, zai yi magana da kai.
34 Sai Bitrus ya bude bakinsa ya ce, “Gaskiya, na fahimci Allah baya nuna bambanci.
35 Maimakon haka, cikin kowace al'umma duk mai ibada kuma mai aikata adalci karbabbe ne a gare shi.
36 Ku kun san sakon da ya aika wa mutanen Isra'ila, a lokacin da ya sanar da labarin mai kyau na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shine Ubangiji na duka.
37 Ku da kanku kun san al'amuran da suka kasance, wanda ya faru cikin Yahudiya, farawa daga Galili, bayan sanarwar baftismar da Yahaya ya yi.
38 Al'amura game da Yesu Banazare, yadda Allah ya kebe shi da Ruhu Mai Tsarki da iko kuma. Ya kuma ci gaba da aikin alheri da warkarwa ga dukan wadanda shaidan ya daure, domin Allah yana tare da shi.
39 Mu shaidu ne ga dukan abubuwan da ya yi a kasar Yahudawa da cikn Urushalima, wannan Yesu wanda suka kashe, ta wurin giciye shi a akan itace.
40 Wannan mutumin, Allah ya ta da shi rana ta uku ya kuma maishe shi sananne,
41 ba ga dukan mutane ba, amma ga shaidun da Allah ya zaba tun da farko - mu kanmu, wadanda muka ci muka sha tare da shi bayan tashin sa daga matattu,
42 Ya umarce mu mu yi wa mutane wa'azi mu kuma tabbatar cewa shine wanda Allah ya zaba ya yi shariya bisa masu rai da matattu.
Ayyukan Manzanni 10 in Litafi Mai-tsarki