Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 10:29-33 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 10:29-33 in Litafi Mai-tsarki

29 Wannan shine yasa na zo ba tare da musu ba, a lokacin da kuka kira ni. Don haka na tambaye ku me ya sa kuka aika in zo.”
30 Karniliyas ya ce “Kwanaki hudu da sun wuce a daidai wannan lokaci, ina addu'a da cikin sa'a na tara (karfe uku) a gidana, sai na ga mutum tsaye a gabana da tufafi mai haske.
31 Ya ce, “Karniliyas, Allah ya ji addu'ar ka, kuma taimakon ka ga talakawa ya tuna ma Allah da kai.
32 Saboda haka ka aika da wani Yafa, ya kira maka mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus. Yana zama a gidan Saminu majemi, da ke bakin teku.
33 Idan ya zo, zai yi magana da kai.
Ayyukan Manzanni 10 in Litafi Mai-tsarki