Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 10:1-13 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 10:1-13 in Litafi Mai-tsarki

1 An yi wani Mutum a birnin Kaisariya, mai suna Karniliyas, shugaban sojoji ne na kungiyar da ake kira Italiya.
2 Mutum ne mai ibada, wanda ya mika kansa da iyalinsa ga bautar Allah; ya kan bada taimakon kudi mai yawa ga Yahudawa, kuma yana addu'a ko yaushe ga Allah.
3 Wajen sa'a ta tara ga yini, an bayyana masa cikin wahayi mala'kan Ubangiji na zuwa gare shi sai mala'ikan ya ce masa, “Karniliyas!”
4 Karniliyas ya zuba wa mala'ikan ido a tsorace ya ce “Menene, mai gida?” mala'ikan ya ce masa, “Addu'ar ka da taimakon ka ga talakawa ya kai sama matsayin sadaka abin tunawa a gaban Allah,
5 “Yanzu ka aika mutane zuwa birnin Yafa su kawo mutum mai suna Saminu wanda ake kira Bitrus.
6 Yana zama tare da Saminu majemi, wanda gidansa ke bakin teku.
7 Da mala'ikan da ya yi magana da shi ya tafi, Karniliyas ya kira biyu daga barorin gidansa, da kuma soja guda mai bautar Allah daga cikin sojojin da suke masa hidima.
8 Karniliyas ya fada masu dukan abin ya faru sai ya aike su Yafa.
9 Washe gari wajen sa'a ta shida (tsakar rana) suna cikin tafiya da suka yi kusa da birni, Bitrus ya hau kan bene don ya yi addu'a.
10 Sai ya ji yunwa kuma yana bukatar wani abinda da zai ci, amma a yayin da mutanen na dafa abinci, sai ya ga wahayi.
11 Sai ya ga sararin sama ya bude kuma wani tasa na saukowa, wani abu kamar babban mayafi yana saukowa zuwa duniya, ana zuro shi ta kusuryoyinsa hudu.
12 A cikinsu kuwa akwai dukan halitun dabbobi masu kafa hudu da kuma masu rarrafe a duniya da tsunstayen sama.
13 Sai murya ta yi magana da shi; “Tashi, Bitrus, yanka ka ci”
Ayyukan Manzanni 10 in Litafi Mai-tsarki