Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 9

Yahaya 9:31-41

Help us?
Click on verse(s) to share them!
31Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa.
32Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba.
33In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba.”
34Suka amsa suka ce masa, “an haife ka cikin zunubai, yanzu kana so ka yi mana koyarwa?” Sai suka fitar da shi.
35Yesu ya ji cewa sun fitar da shi daga majami'a. Da ya same shi sai ya ce masa, “Kana bada gaskiya ga Dan Allah?”
36Sai ya amsa masa yace, “Wanene shi, Ubangiji, da zan bada gaskiya gare shi?”
37Yesu yace masa, “Ai ka gan shi, shine wanda yake magana da kai.”
38Mutumin ya ce, “Ubangiji, Na bada gaskiya.” Sai ya yi masa sujada.
39Yesu ya ce, “Don hukunci na zo wannan duniya domin wadanda ba su gani su gani, saboda kuma wadanda suke gani su zama makafi.”
40Wadansu Farisawa wadanda suke tare da shi suka ji wadannan abubuwan, suka tambaye shi, “Muma makafi ne?”
41Yesu ya ce masu, “Inda ku makafi ne, da ba ku da zunubi, amma yanzu kun ce, 'Muna gani', don haka zunubinku ya tabbata.

Read Yahaya 9Yahaya 9
Compare Yahaya 9:31-41Yahaya 9:31-41