Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Yahaya - Yahaya 9

Yahaya 9:1-32

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa.
2Sai almajiransa suka tambaye shi, “Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?”
3Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa.
4Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki.
5Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya.”
6Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar.
7Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike).” Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani.
8Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, “Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?”
9Wadansu suka ce, “shi ne.” Wadansu suka ce, “A'a, amma yana kama da shi.” Amma shi ya ce, “Ni ne wannan mutum.”
10Suka ce masa, “To yaya aka bude maka idanu?”
11Sai ya amsa, “Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani.”
12Suka ce masa, “Ina yake?” Ya amsa, “Ban sani ba.”
13Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa.
14A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu.
15Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, “Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani.”
16Wadansu daga cikin farisawa suka ce, “Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. “Wadansu suka ce, “Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?” Sai rabuwa ta shiga tsakanin su.
17Sai suka tambayi makahon kuma, “Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?” Makahon ya ce, “shi annabi ne.”
18Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin.
19Su ka tambayi iyayen, “Wannan shine yaronku da kuka ce an haife shi makaho? Yaya yanzu ya ke iya gani?”
20Sai iyayen suka amsa masu, “Mun san wannan yaronmu ne kuma a makaho aka haife shi.
21Yadda ya ke gani yanzu, bamu sani ba, kuma wanda ya bude masa idanu, bamu sani ba. Ku tambaye shi, ba yaro ba ne. Zai iya magana don kansa.”
22Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a.
23Domin wannan ne, iyayensa suka ce, “Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, “Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne.”
25Sai wannan mutum ya amsa, “Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani.”
26Sai su ka ce masa, “Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?”
27Ya amsa, “Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne?
28Sai suka kwabe shi suka ce, “kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne.
29Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba.”
30Mutumin ya amsa masu ya ce, “Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu.
31Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa.
32Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba.

Read Yahaya 9Yahaya 9
Compare Yahaya 9:1-32Yahaya 9:1-32